
Nijer ta fara aiwatar da dokar hana ‘yan Nigeria shiga da fasfon kungiyar Ecowas ta bukaci komawa amfani dana kasa da kasa.
Wannan matakin ya biyo bayan ficewar kasar daga kungiyar tare da Mali da kuma Burkina Faso a karshen shekara da ta gabata.
Duk da bude kan iyakokin Nijar da Najeriya, hukumomin kasarta Nijar na ci gaba da daukar sabbin matakai ga masu son shiga musamman daga Najeriya ta iyakokin Illela dake nan Najeriya da Konni kuma dake can kasar ta Nijar.
‘Yan kasuwan da ke amfani da iyakokin da sauran matafiya a yanzu na ci gaba da fuskantar matsaloli yayin da hukumomin Nijar suka ki amincewa da fasfon ECOWAS a matsayin shaida ta hakika ga ‘yan Najeriya.
A cewar wata majiya daga yankin Tawa a Jamhuriyar Nijar, tuni jami’an kan iyaka sun fara mayar da mutanen da suka dogara kawai da fasfo din kungiyar ECOWAS a matsayin shaida.
