
Duniya ta kwallo kafa ta shiga cikin alhini bayan samun labarin mutuwar Diogo José Teixeira da Silva, wanda aka fi sani da Diogo Jota, ɗan wasan gaba na Liverpool da kuma ƙungiyar ƙasar Portugal.
Jota ya rasu yana da shekaru 28, sakamakon wani haɗarin mota da ya auku a yammacin ƙasar Spain.
Ɗan wasan ƙwallon ƙafar Liverpool kuma ɗan ƙasar Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a birnin Zamora, ƙasar Spain.
A cewar wani rahoto, marigayinn na tare ɗan uwansa Andre Felipe a wata motar alfarma kirar Lamborghini a yayin da hatsarin ya faru.
Motar ta kauce daga hanya ne bayan tayarta ta fashe yayin da suke ƙoƙarin wuce wata mota a gabansa.
Nan take motar ta kama da wuta wanda hakan ya yi ajalinsu.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare agogon Sifaniya.
Rasuwarsa ya girgiza duniyar wasanni, musamman masoya ƙwallon kafa da magoya bayan Liverpool, inda ake ci gaba da aika saƙon ta’aziyya ga iyalansa da ƙungiyarsa.
Rahotannin da jaridar wasanni ta ƙasar Spain, MARCA, ta fitar sun bayyana cewa haɗarin ya rutsa da Jota ne tare da ɗan uwansa, kuma ya mutu nan take a cikin motar, kwanaki kalilan bayan da ya ɗaura aure.
Wannan mummunar al’amarin ya auku ne a daidai lokacin da Jota ke samun ci gaba mai ƙayatarwa a sana’ar sa ta ƙwallon ƙafa.
An haifi Diogo Jota a ranar 4 ga Disamba, 1996, a birnin Porto na ƙasar Portugal.
Sana’ar sa ta kwallon kafa ta ɗauki hankalin duniya tun bayan da ya fara fitowa a manyan ƙungiyoyi, kafin daga bisani ya koma Liverpool daga Wolverhampton Wanderers a ranar 19 ga Satumba, 2020.
A nan, ya zama ɗaya daga cikin ginshiƙai a ɓangaren gaba, yana taka rawa tare da manyan ‘yan wasa kamar Mohamed Salah da Darwin Núñez.
Rasuwar Jota ta bar babban gibi ba kawai a zuciyar magoya bayan Liverpool da Portugal ba, har ma a tsakanin ‘yan wasa, masu horarwa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wasanni gaba ɗaya.
Tuni dai sakonnin ta’aziyya daga manyan kungiyoyi, shugabanni da masoya suka fara kwaranya, suna addu’a ga iyalan mamacin da kuma ƙungiyar Liverpool da ƙasar sa ta Portugal.