Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano AKTH.
A cewar data daga cikin daraktocin hukumar, Dakta Salahudeen Sikiru, hakan wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da hukumar ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman.
“An fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar.
“A karkashin shirin, yara da ke fama da matsalolin gaggawa kamar rashin numfashi da amosanin jinni da cutar shawara da yaran da aka haifa bakwaini da ma cututtukan da ke buƙatar tiyata za su samu kulawa kyauta.” In ji shi.
Daraktan ya kara da cewa, duk yaron da ya samu kulawar gaggawa, za a saka shi cikin shirin Inshorar Lafiya na NHIS, inda hukumar za ta ci gaba da biyan kudin inshorar don tabbatar da samun kulawar lafiya mai inganci.
