Ahmad Hamisu Gwale
Hukumar shirya gasar kwallon kafa ta Najeriya, ta bayar da hutun rabin kaka a gasar Firimiyar Najeriya ta NFPL.
Hukumar ta bayar da hutun ne ga kungiyoyi 20 da suke fafata gasar, domin hutun rabin kaka, baya ga damar daukar yan wasa daga ranar 5 zuwa karshen watan Janairu.
Ana saran dawowa ci gaba da fafata a gasar a ranar, 25 ga Janairu, da kawo yanzu haka Remo Stars na kasancewa a matakin farko da maki 36.
Gasar ta NFPL dai tuni aka kammala zagayen farko na gasar ta kakar wasannin shekarar 2024/2025 da Rivers United zuwa yanzu tana mataki biyu a jerin teburi.
Kano Pillars da ke karkashin jagorancin Usman Abdallah na mataki na Takwas da maki 25 a wasanni 18 da ta fafata, kuma zata buga wasa da Enyimba a wani kwantan wasan hammayya da kungiyoyin zasu kece raini da juna.