Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta raba kayan tallafi ga ’yan kasuwar waya ta Farm Center da gobara ta shafa.
Hakan na cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi.
An gudanar da rabon kayan agajin ne a rumbun ajiyar hukumar da ke kan titin Maganda a Karamar Hukumar Nassarawa.
“Tallafin na da nufin rage radadin asarar da ’yan kasuwar suka yi, tare da taimaka musu wajen farfadowa daga asarar gobarar.
“Ina mai kira da a kara daukar matakan kare afkuwar gobara a kasuwanninmu”. In ji sanarwar.
Rabon kayan ya samu halartar Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Tarauni Muntari Yarima da takwarar hukumar a Kano SEMA, da Ƙungiyar Agaji Ta Red Cross da NSCDC da kuma shugabannin ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a jihar
