
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen Jihar Gombe ta bayyana lalata wata babbar gonar tabar wiwi da ke Karamar Hukumar Kaltungo, a wani yunkuri na dakile yaduwar miyagun kwayoyi a jihar.
Kwamandan NDLEA a Gombe, Mallam Maijama’a Muhammad, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar kulla zumunci da ya kai wa Darakta-Janar na Gombe Media Corporation (GMC), Ibrahim Isa.
A cewarsa, hukumar ta kama miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira tsakanin watan Yuni zuwa Agusta na shekarar 2025.
Muhammad ya kara da cewa an kama mutum 69 maza da mata da suka yi yunkurin shigar da miyagun kwayoyi cikin jihar a lokuta daban-daban.
Ya bayyana cewa NDLEA na amfani da dabarun rage samarwa da rage bukatar kwayoyi, tare da fadakar da al’umma game da illolinsu.
A nasa jawabin, Darakta-Janar na GMC, Ibrahim Isa, ya tabbatar da goyon bayan kafar yada labaran ga NDLEA, ciki har da bayar da lokacin watsa shirye-shirye kyauta don wayar da kan jama’a.
Ya kuma yi alkawarin ci gaba da yin aiki tare da hukumar domin yakar ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.