
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano ta cafke wani mutum mai shekara 37 da kama kwalabe 8,000 na Akuskura da kuma sinki 48 na tabar wiwi.
Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sadiq Muhammad Maigatari ya fitar ranarTalata.
Mai gatari ya kuma ce an cafke wanda ake zargin mai suna Ali Muhammad ne a kan titin Zariya zuwa Kano kusa da gadar Tamburawa.
Hukumar ta bukaci jama’a da su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishinta mafi kusa ko kuma wata hukumar tabbatar da doka da oda.