
Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) anan Kano sun kama buhu uku na tabar wiwi mai nauyin kilo 112, bayan wani hatsarin mota da ya faru a Gadar Tamburawa, kan hanyar Zariya.
Hatsarin ya faru ne a ranar Asabar, lokacin da wata motar Golf ta yi karo da babbar mota.
Sanarwar da Kakakin hukumar Sadiq Mai Gatari ya fitar ta bayyana cewa jami’an NDLEA sun garzaya wurin, suka ceto direba da fasinja daga cikin Golf, inda ɗaya daga cikinsu ya yi yunkurin guduwa amma aka cafke shi.
Direban motar ya amsa ya kanyi irin wannan jigila anan Kano da wasu jihohi.
A halin yanzu direban Golf na karɓar magani yayin da ake cigaba da yi masa tambayyoyi.