
Sanata Natasha a zauren Majalisar Dinkin Duniya yayi gabatara da koken
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ƙarar Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio da kuma Majalisar ta Najeriya ga Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ta gabatar da karar ne ta fuskar koke a zaman taron mata da aka gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a birnin New York a Amurka.
Sanata Natasha Akpoti-Uguaghan ta yi kira ga majalisar ta hukunta Majalisar Dattawan Najeriya game da dakatarwar da aka yi mata na tsawon wata shida.
Natasha ta ce, dakatar da ita daga Majalisar Dattawan Najeriya da aka yi ba bisa ƙa’ida ba ne, kuma ta nuna damuwa kan cewa za a iya ƙoƙarin tsare ta saboda yin magana a fili.
Natasha ta koka cewa tana fuskantar “tsangwama a siyasa da kuma barazana” saboda ta nemi a yi bincike na gaskiya kan zarge-zargen cin zarafi ta hanyar neman yin lalata da ta yi wa Akpabio.
Majalisar dattawan ta dakatar da sanata Natasha ne kan zargin yunurin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio.

Inda tace ta yi kiran ne don “kada duniya ta zura ido a yi shiru yayin da dimokraɗiyya da haƙƙoƙin mata ke cikin tasku a Najeriya”.
Tun farko dai Sanata Natasha ta fito ta bayyana zarge-zargen ne bayan da a wani zaman majalisa aka ga yadda take ɗaga murya tana nuna fushinta game da yadda aka sauya mata wajen zama a majalisar ba tare da wani dalili ba, a cewarta