
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bayyana muhimmancin nasararsa a zaben 2023 ga tarihin kasarnan da ikirarin cewa tarihin Najeriya da bai cika ba da bai yi nasara a zaɓen 2023 ba.
Tinubu ya faɗi haka ne a ranar Lahadi a garin Ijebu Ode a Jihar Ogun yayin gudanar da addu’o’in kwana Takwas na rasuwar sarkin garin Ijebu Oba Sikiru Adetona.
Shugaban ya yaba wa marigayin bisa goyon baya da albarkar da ya masa kafin zaɓen 2023. A inda yay i ma sa albishirin lashe zaben
“Za ka ci zaɓen nan, kuma za ka sake nasara a wani karon.” In ji Sarkin ga Tinubu a yayin ziyarar da ya kai masa a yawon Kamfe gabannin zaben.
Tinubu ya kuma ce, marigayin ya taka rawa sosai wajen ganin an samu dimokuraɗiyya a Najeriya, musamman a lokacin fafutukar ranar 12 ga watan Yuni.
Ya kuma kara da bayyana Sarkin a matsayin mai hikima da jajircewa da kuma shugabanci na gari.
Har ila yau, Tinubu ya gode wa Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, bisa rawar da ya taka lokacin jana’izar Sarkin.
Gwamna Abiodun, ya buƙaci al’ummar Ijebu da su zauna lafiya, su ci gaba da rayuwa bisa haɗin kai da zaman lafiya kamar yadda Sarkin ya koyar da su.