
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce yana sa ran jam’iyyar APC za ta mamaye jihohi 30 cikin 36 da ke ƙasar nan kafin shekarar 2026.
Ya bayyana haka ne a lokacin taron dabarun aiki na watanni uku-uku na shekarar 2025 na ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC wanda aka gudanar a Maidugurin jihar Borno.
Yayin taron da ya mayar da hankali kan yadda za a inganta haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin da APC ke mulki, ministan ya ce yawaitar sauya sheka zuwa APC na faruwa ne saboda kyawawan manufofi da shirye-shiryen shugaba Tinubu.
Ya ce hakan ya haifar da ingantaccen mulki, gyaran tattalin arziki da daidaituwar darajar Naira.