
Wani soja rike da tutar kasar a fadar shugaban kasar da aka ragargaje
Daga Saddam Musa Khalid
Kungiyar ‘yan asalin sudan mazauna jihar Kano mai suna ‘Ihsan Family Group’ sun yi kira ga gwamnatin tarrayya da ta sa baki don kawo karshe zub da jinin da ake yi a Sudan.
Kungiyar ta yi wannan kira ne a yayin gudanar da taron sada zumunci da ta ke yi a duk shekara a ranar Laraba a gidan Ahmad Dubai dake unguwar Tarauni a Kano.

A hirar wakilinmu da Shugaban kungiyar a Kano, Mukhtar Adam Ibrahim ya ce, taron na bana ya maida hankali ne kan matsalar yakin cikin gida a yanzu.
“Muna bukatar gwamnatin kasar nan da ta kaiwa kasar Sudan dauki domin kawo karshen yakin da ake ciki”. In ji shi.
Yanzu an shafe shekaru uku kenan ana gwabzawa fada tsakanin sojojin kasar da mayakan RSF, wanda hakan ya jefa rabin al’ummar kasar cikin mawuyacin hali da suke bukatar agaji.

Taron kungiyar na zumunci ne da taimakon juna ya samu halartar Iyaye maza da mata Sudanai mazauna Kano da kewaye.
Wasu daga cikin wadanda suka halacci taron sada zumuncin sun bayyana farin cikinsu ta yadda taron kan hada kansu guri guda.
“ ‘yan asalin sudan din da ke zaune a kasar na ci gaba da hada kansu domin taimakekeniya ta yadda za’a gudu tare a tsira tare.” In ji Sakatariyar Kungiyar Habiba Ramdan Mu