
Babban Jirgin ruwan dakon Man fetur
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa Nijeriya ta shigo da tataccen man fetur da ya kai naira tiriliyan 12.48 a shekarar 2024.
Rahoton ya nuna cewa an shigo da fetur na naira tiriliyan 2.63 a kashi na farko na shekarar. A kashi na biyu, an shigo da tiriliyan 3.22, sai tiriliyan 3.32 a kashi na uku, da kuma tiriliyan 3.3 a kashi na huɗu.
Jimillar cinikayyar da Nijeriya ta yi da ƙasashen waje ta kai naira tiriliyan 138. Daga ciki, an kashe naira tiriliyan 60.5 wajen shigo da kayayyaki, yayin da aka samu naira tiriliyan 77.4 daga fitar da kaya.
Tataccen man fetur ne ya fi yawa cikin kayayyakin da Nijeriya ke shigo da su. A gefe guda, ɗanyen mai ne ya fi rinjaye cikin kayayyakin da ake fitarwa zuwa ƙasashen waje.

Duk da kasancewar Nijeriya tana da arzikin danyen mai, har yanzu ana shigo da tataccen fetur daga waje. Wannan na da nasaba da ƙarancin matatun mai da ke aiki a ƙasar.
Ana sa ran shigowar sabbin matatun mai, kamar na Dangote, zai rage dogaro da man fetur daga ƙasashen waje tare da tasiri kan tattalin arzikin ƙasa.