Gwamnatin Tarayyar ta musanta hakan ne da kakkausar murya bayan zargin da aka yi mata na hannu a cikin Lamarin.
Cikin wata sanarwa da Alkasim Abdulkadir Maitamaki na musamman ga Ministan kasan waje na Nijerya kan harkokin Labarai ya fitar a makon nan ta musanta labarin.
Yace Ambassada Yusuf Maitama Tuggar OON yace zargin da hukumomin Nijar suka yi na cewa Yan ta’addar Lakurawa sun aikata laifin ba gaskiya bane.
Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar, tare da taimakon jami’an tsaron kasashen waje, ciki har da Najeriya aka zarga da kai harin a Niger-Benin kan bututun mai a ranar 13 ga Disamba 2024, a Gaya, yankin Dosso Jamhuriyar Nijar.
Tuni Gwamnatin Najeriya ta jajantawa gwamnatin Nijar kan mummunan harin da aka kai kan bututun mai, amma ya sanar da cewa Masu aikata laifin ba su da goyon baya ko taimako daga Najeriya.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kuma nuna damuwa na yadda sarai cewa babu sojojin Faransa dakaru a yankin arewacin kasar da ke shirin tada zaune tsaye gwamnatin Nijar.
Yana mai cewa Wadannan zarge-zarge ba su da tushe ballan tana makama gaba daya.