Me martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni waɗanda ba su da nagarta, wanda hakan ne matsalar da take hana kasar ci gaba.
Sarkin ya bayyana haka ne a bikin Kano International Poetry Festival da aka yi a Kano.
Sarkin ya ce matsalolin ƙasar nan sun samo asali ne daga rashin shugabanci na gari.
Sanusi ya roki matasa da su tashi tsaye su ɗauki ragamar shugabanci daga hannun tsofaffin da suka daɗe suna riƙe da mulki.
Ya kuma kare cire tallafin man fetur, inda ya ce Najeriya da ta ci gaba da biyan tallafin da tuni ƙasar ta yi rauni.
Ya bayyana cewa tallafin man bai amfanar da Najeriya ba, face ƙara bunƙasa masana’antun ƙasashen waje maimakon a gyara na cikin gida.
Sanusi ya kuma yi gargaɗin cewa yawan karɓo bashi da kuma ɓatar da shi da gwamnati ke yi zai iya jefa tattalin arziƙin Najeriya cikin mawuyacin hali a nan gaba.
