
Tsohon shugaban ƙasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya bayyana cewa Najeriya ba za ta sake komawa tsarin mulkin soja ba, yana mai jaddada cewa dimokuraɗiyya ita ce hanya mafi dacewa don ci gaban ƙasa.
Gowon ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin ƙaddamar da littafi mai taken “Military Factor in Nigerian History, 1960–2018”, wanda aka wallafa domin tunawa da cika shekaru 70 da kafuwar Ƙungiyar Tarihi ta Ƙasa (Historical Society of Nigeria).
A cewarsa, duk da irin gudunmawar da sojoji suka bayar a tarihin ƙasa, musamman a lokacin yakin basasa da kuma wajen samar da ababen more rayuwa, bai su kamata su sake tsoma baki a harkokin siyasa ba.
Ya kuma ce, tsarin mulkin soja, a wasu lokuta, na tauye haƙƙin jama’a da hana ci gaban dimokuraɗiyya.
“Duk da kurakuran da ke tattare da dimokuraɗiyya, ita ce hanya mafi inganci da ta dace da ƙasa mai tarin bambance-bambance kamar Najeriya.
“Akwai buƙatar rundunar soji ta ci gaba da mai da hankali kan kare ƙasa, bunƙasa fasaharta, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin farar hula don samar da zaman lafiya da daidaito. In ji Gowon.
Littafin da aka ƙaddamar ya samu yabo daga masana, inda suka bayyana shi a matsayin cikakken tarihin tasirin rundunar soji a siyasar Najeriya, tattalin arziƙi da zamantakewa tun daga 1960 zuwa 2018.