Wasu dattawa biyu ‘yan arewa sun kaddamar da wata sabuwar tafiyar matasa don ceto arewa daga halin da ta ke ciki na siyasa da koma baya a tattalin arziki.
Fitacciyar ’yar gwagwarmayar siyasa Hajiya Naja’atu Muhammad da tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa ne suka kaɗɗamar da sabuwar tafiyar matasa domin ceto yankin daga halin da ta ke ciki a siyasance.
A ranar Talata ne manyan ’yan siyasar suka ƙaddamar da tafiyar matasan da nufin tallafa musu wajen ganin an lalubo mafita daga matsalolin siyasa da tattalin arziki da suka dabaibaye yankin.
“Lokaci ya yi da matasa za su karɓi jagoranci, kuma idan aka ba su dama, za su taka rawar gani, muddin su ka samu gogaggun dattawa da ke ɗora su a kan hanya” inji tsohon gwamna kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar DPP Attahiru Bafarawa a shekarar 2015.
“Wannan ƙungiyar ba ta siyasa ba ce, kuma za ta mayar da hankali ne kawai wajen tallafawa matasa da kawo ci-gaba a yankin arewacin kasar nan” inji Hajiya Naja’atu Muhammad.
Kungiyar mai suna ‘Northern Star Youth Movement Initiative’, na shirin buɗe rassa da ofisoshi a faɗin yankin arewa, domin ba su dama da abubuwan da suke buƙata.
Da kuma taka rawar siyasa a yankin.