
Alhaji Ahmed Bello Isa mahaifin marigayi Bilyaminu Bello wanda Maryam Sanda ta kashe, ya ce shi ya amince da yafiyar da shugaban ƙasa Tinubu ya yi wa surukarsa.
Mahaifin marigayin ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Talata.
“Mu a matsayinmu na Musulmi muna karɓar duk abin da ya fito daga Allah Madaukakin Sarki. Na yafe mata kuma bani da wata ƙiyayya ga Gwamnatin Tarayya ko danginta. Domin ba za ta dawo da ɗana ba, amma yafiya tana kawo salama,” in ji shi.
Bello ya bayyana cewa roƙonsa na neman afuwa ga Maryam ya fara ne tun daga shekara ta 2019, kafin ma kotu ta yanke mata hukuncin kisa.
A inda ya ce, ya rubuta wasiku da dama ga hukumomi, ciki har da tsohon Babban Lauyan Ƙasa Abubakar Malami, da kuma Kwamishinan ’Yan sanda na Babban Birnin Tarayya, yana neman sassauci ga surukarsa.

A ranar Litinin ne Dakta Bello Mohammed ya fitar da wata sanarwa a madadin wasu ’yan uwan marigayin da ta soki yafiyar da shugaban ƙasa ya bayar, yana mai cewa, “wannan shi ne mafi muni na rashin adalci da kowanne iyali zai iya fuskanta.”
Amma a martaninsa, Mahaifin Bunyamin ya yi watsi da wannan sanarwa, yana mai cewa bai ta wakilci ra’ayinsa ba.
“Wannan ra’ayinsu ne na kansu. Ni ne uban mamacin, kuma na zaɓi yafiya. Ba lallai ne kowa ya duba abu iri ɗaya ba, amma ina ganin wannan shi ne sahihin hanya, don samun salama, don yaran, da don neman rahamar Allah,” in ji shi.
Kotu ta samu Maryam Sanda ne da laifin kisan mijinta, Bilyaminu Bello, wanda shi kuma ɗan’uwan tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa ne, Alhaji Bello Haliru Mohammed ne. An kuma yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a watan Janairu na shekara ta 2020.
Kisan ya faru ne a watan Nuwamba 2017 sakamakon rikicin cikin gida tsakanin ma’auratan biyu a Abuja.
Ya tayar da kura a fadin ƙasar nan tare da jawo hankalin jama’a kan batutuwan tashin hankali a tsakanin ma’aurata da kuma neman adalci.