Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Hulɗa da Jama’a, Fatima Sanda Usara, ta fitar a ranar Juma’a.
A cewar hukumar, sauye-sauyen sun haɗa da mayar da ma’aikatan da aka aro daga wasu ma’aikatu zuwa inda aka samo su a asali, domin rage yawan ma’aikatan da ke gararamba da kuma sake fasalin tsarin aiki.
Takardun komawar ma’aikatan an raba su ne a ranar Alhamis, 4 ga Satumba, 2025.
Haka kuma, hukumar ta amince da Karin girma ga wasu ma’aikata da suka cancanta,Shirye-shiryen horaswa da bunkasa kwarewa ga dukkan ma’aikata domin ƙara inganta basira da ilimi a wajen aiki.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya jaddada cewa NAHCON za ta ci gaba da gina ƙwararrun ma’aikata masu jajircewa domin tabbatar da cika nauyin da dokar ƙasa ta dora mata, na hidimtawa Alhazan Najeriya.
