Babban Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce sojojin Najeriya sun samu bayanan karya daga fararen hula kafin harin kisan gillar da ya faru a jihar Benue.
Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, Janar Musa ya bayyana cewa a ranar da harin ya faru, an shaidawa sojojin da ke garin Yelewata cewa wani kauye daban yana fama da hari.
Ya ce sojojin da ke Yelewata sun nufi kauyen da aka ce an kai masa hari, sai kuma masu kai harin suka kutsa Yelewata suka kashe jama’a.
Shugaban tsaron ya zargi wasu mazauna yankin da bayar da bayanai ga ‘yan ta’adda dangane da motsin dakarun soji.
A ranar 14 ga Yunin da muke ciki ne dai wasu ‘yan bindiga suka kai mummunan hari kan al’ummomin Yelewata da Daudu da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue, inda aka kashe fiye da mutane 200.
