Aminu Abdullahi Ibrahim
Mutane kusan 20,000 sun nemi guraben aikin koyarwa 4,000 a Jigawa
Ba ƙasa da yan takara 19,966 suka nemi shiga shirin J-TEACH Batch C na Jihar Jigawa, yayin da ake sa ran za a tantance mutane 4,000 kawai.
Shugaban Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta Jihar (SUBEB), Farfesa Haruna Musa, ne ya bayyana hakan, inda ya ce shirin na shekaru biyu ne domin horar da malamai, tare da inganta ingancin koyarwa a jihar.
A cewarsa, daga cikin masu neman guraben, akwai maza marasa aure 7,450, maza masu aure 5,433, da mata marasa aure 2,503, yayin da ake ci gaba da tattara bayanan mata masu aure.
