Firayiministar Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo Judith Suminwa ta bayyana cewa, rikicin da ke ci gaba da ƙamari a Gabashin ƙasar ya yi sanadin mutuwar mutane 7,000.
Fiye da 500,000 kuma sun rasa matsugunansu bayan hare-haren da suka lalata sansanonin ‘yan gudun hijira.
Shugabar ta bayyana hakan ne a taron Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta MDD a Geneva, a inda ta jaddada irin mawuyacin hali da miliyoyin jama’ar kasar ke ciki.
A nasa jawabin Babban Sakataren Majalisar Antonio Guterres, ya yi kira da a kawo ƙarshen zub da jinni kasar.
Rikicin na ƙara tsananta, tare da take haƙƙin ɗan adam daga hannun ‘ƴan tawayen M23 da ake zargin suna samun goyon bayan Rwanda.
Ƙungiyar M23 ta kwace yankuna da dama, ciki har da Goma da Bukavu, abin da ke ƙara barazanar faɗaɗa rikicin.
MDD na kira ga ƙasashen duniya da su gaggauta ɗaukar matakan kawo ƙarshen tashin hankalin da ya jefa fararen hula cikin kunci.
