
Majalisar Wakilai ta Najeriya ta bayyana girman iftila’in ambaliyar ruwa da ya afku a Mokwa, jihar Neja, da wasu sassan ƙaramar hukumar Edu a jihar Kwara, inda fiye da mutane 600 suka ɓace sakamakon tsananin bala’in ambaliyar ruwan saman da ya afku.
Dan majalisa Joshua Audu Gana daga Neja da Saba Ahmed Umaru daga Kwara sun gabatar da ƙudiri na gaggawa a zaman majalisar a ranar Laraba, inda suka bayyana cewa mutane 500 ne aka tabbatar sun mutu, yayin da fiye da 600 suka ɓace kuma ba a gano su ba har yanzu.
Ana hasashen ambaliyar ta faru ne sakamakon rugujewar tsohuwar gadar jirgin ƙasa ta Mokwa, wanda ya haifar da mamayar ruwa a muhimman yankunan kasuwanci da gidaje na jihar.
Rahoton ya ƙara da cewa gidaje fiye da 4,000 sun lalace, mutane 200 kuma sun jikkata, yayin da filayen gona da ababen more rayuwa da dama sun rushe, lamarin da ya jefa dubban jama’a cikin halin neman agaji.
Majalisar ta nuna damuwa kan barazanar kamuwa da cututtuka kamar kwalara, typhoid da gudawa mai tsanani, sakamakon gurɓacewar ruwa da rashin tsafta a sansanonin da aka ajiye waɗanda suka rasa muhallansu.
Majalisar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa Ta Ƙasa (NEMA) da su gaggauta samar da kayan agaji da na tsaftace ruwa domin rage barazanar yaduwar cututtuka.
Haka kuma, an buƙaci a inganta tsarin kariya daga ambaliya da kuma gina sabbin ababen more rayuwa a yankunan da abin ya shafa.