
Rundunar ƴansandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta tabbatar da mutuwar mutane shida da ƙonewar motoci 14 bayan da wata babbar motar ta kama da wuta a yankin Karu.
Kakakin rundunar ƴansandan SP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce, ibtila’in ya faru ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe 6:58 na yamma bayan wata babbar mota da ke maƙare da siminti ta faɗa kan motocin da ke maƙale cikin cunkoso ababen hawa kusa da gadar Nyanya.
Ta ce ma’aikatan ceto sun yi gaggawar isa wurin da ke cike da baƙin hayaƙi da tsananin zafi domin ceto waɗanda suka maƙale inda tare da zaƙulo mutane shida, sai dai bayan kai su asibiti likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
Kakakin rundunar ta kuma ce, da haɗin gwiwar ƴansanda da ma’aikatan kashe gobara da ma wasu jam’ian tsaro an samu nasarar kashe gobarar.
Rundunar ƴansandan Abuja ta kuma miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda iftila’in ya shafa tare da tabbatarwa da alumma cewa za a gudanar da cikakken bincike kan sanadin iftila’in.
Ita ma Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce, akwai mutanen da ba san adadin su ba dake kwance a wasu asibitocin Abuja domin samun kulawar likitoci.