Rikici tsakanin Makiyaya da Manoma ya haddasa asarar rayukan mutane 56 cikin makon guda a jihar Benue.
Alƙaluman da mahukuntan jihar suka fitar a ranar Asabar gabanin ziyarar tawagar Gwamnan zuwa yankin ya ce, mutane 17 ne suka mutu a hare-haren da ɓangarorin biyu suka kai wa junansu.
A cewar hukumomin jihar galibi manoma kan fuskanci makamantan hare-haren daga takwarorinsu makiyaya wanda a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka.
Mai taimakawa Gwamnan Benue kan al’amurran yaɗa labarai Solomo Iorpev ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, bayan ziyartarsu sun gano cewa adadin ya wuce 17 da suka sanar a farko ta yadda a yanzu aka ƙirga gawarwakin mutane aƙalla 56 wasu da dama kuma suka jikkata.
Rikici tsakanin Makiyaya da Manoma ba sabon abu ba ne a jihar ta Benue, wanda a lokuta da dama ke haddasa asarar ɗimbin rayuka tare da juyewa a wasu lokutan zuwa rikici mai alaƙa da ƙabilanci ko kuma addini.
Gwamnan Hyacinth Alia ya ɗora alhakin hare-haren makon da muke bankwana da shi kan tsagerun ƴanbindigar da suka fito daga ƙananan hukumomin Ukun da Logo.
