Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta, bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da maza da mata da yara ta faɗo daga saman karyayyiyar gadar, ta nutse a cikin ruwa.
Wani ɗan uwan amaryar, Babangida Halifa Ibrahim Fass, wanda ya rasa ’yan uwa a cikin hatsarin, ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da ake kai ’yar uwarsa amarya gidan mijinta da ke Jega a Jihar Kebbi.
Ya ce, Motar ta faɗo ne daga kan gada ta nutse a ruwa. Da aka ciro su, mutum 19 daga cikinsu sun mutu, maza, mata da yara.
A yau Lahadi ake sa ran yin jana’izar su, kuma an bayyana cewa mahaifin amaryar shi ne tsohon ɗan majalisar jihar, Marigayi Sheikh Dauda Fass.
