Masu zaɓe a Uganda sun fara kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen ƙasar, inda Shugaba Yoweri Museveni ke neman wa’adi na bakwai, bayan kusan shekaru 40 a kan mulki.
Fiye da ‘yan Uganda miliyan 20 ne ke kada kuri’ar a ɗaya daga cikin zabukan da duniya ke sa ido sosai.
Babban mai ƙalubalantar Museveni shi ne sanannen mawaki da ya koma ɗan siyasa, Robert Chagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine, wanda ke fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa karo na biyu.
Ana sa ran hukumar zaɓe ta bayyana sakamakon farko zuwa ranar Asabar da rana.
Ofishin kare hakkin ɗan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa kan yanayin zaɓen, inda ya ce “ana gudanar da zaɓen ne cikin yanayi na tsoro da fargaba,” yayin da aka tsare daruruwan magoya bayan ɗan hamayya kafin zaɓen.
Hukumomin Uganda kuma sun katse hanyoyin intanet a faɗin ƙasar, suna mai cewa hakan na da alaƙa da damuwa kan yaduwar bayanan ƙarya da kuma tashin hankali.
