Ƴan majalisar wakilai na NNPP 13 a Kano sun karyata jita-jitar komawa APC tare da jaddada biyayya ga Kwankwasiyya
Mambobi 13 na jam’iyyar NNPP a majalisar wakilai sun karyata jita-jitar cewa suna shirin komawa APC, bayan sauya shekar ‘yan majalisa biyu daga Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa da kuma Sagir Koki.
‘Yan majalisar sun bayana hakan ne a wata sanarwa da suka fitar a ranar Juma’a.
“Maganar cewa dukkaninmu za su bi sahu ba gaskiya ba ne, muna mai jaddada cewa muna nan daram a NNPP da tafiyar Kwankwasiyya ta Rabiu Musa Kwankwaso.
“Jita-jitar sauya shekarmu daga ‘yan adawa ne da ke jin tsoron karfin jam’iyyarmu, hulɗarmu da ‘yan sauran jam’iyyu ba alamar sauya sheka ba ce, illa dai aikin haɗin kai don ci gaban ƙasa”. In ji sanarwar.
‘Yan majalisar sun kuma kara da cewa babu farfaganda da za ta girgiza biyayyarsu ga NNPP da akidar Kwankwasiyya, inda suka yi alkawarin ci gaba da aiki domin ingantaccen mulki, ilimi, kiwon lafiya, da walwalar ‘yan Najeriya.
Daily Nigerian ta rawaito cewa, mambobin da suka sanya hannu kan sanarwar sune, Garba Diso da Ghali Tijjani da Rabi’u Yusuf da Abdulhakeem Ado da Hassan Danjuma da Muhammad Shehu da Datti Yusuf da Sani Wakili da DanKawu Idris da Tijjani Jobe da Hassan Hussain da Mukhtar Yarima da kuma Muhammed Chiroma.
