Reshen jam’iyyar PDP mai adawa da Abdulrahman Mohammed ke jagoranta tare da samun goyon byan Nyesom Wike ya zaɓi Mao Ohabunwa a matsayin shugaban kwamatin amintattun jam’iyyar.
Tsagin jam’iyyar ya zaɓi Mao ne bayan wani biki da aka gudanar a ofis ɗin hukumar kula da birnin Abuja FCTA a ranar Juma’a.
Ministan Abuja Nyesom Wike, shi ne jagoran tsagin da ke adawa da shugabancin jam’iyyar na asali kuma shi ne ya jagoranci kafa kwamatin inda suka naɗa Isa Dansidi a matsayin sakataren kwamatin.
Da yake jawabi bayan rantsar da kwamatin, Abdulrahman ya ce tsohon kwamatin da Sanata Adolphus Wabara ke jagoranta ya tashi daga aiki.
- PDP ta sanar da ɗage tantance ƴan takarar shugabancin jam’iyyar
- Hukuncin kotu ba zai hana mu gudanar da babban taron ba-PDP
Rukunin da ke yi wa Wike biyayya ya ɗauki wannan mataki ne bayan kwamatin gudanarwa na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa Iliya Damagun ya dakatar da sakatarenta Anyanwu da wasu muƙarraban Wike.
Bayan haka ne kuma su ma ɓangaren Wike suka yi taron manema labarai tare da sanar da dakatar da Damagun da wasu manyan shugabanni.
PDP ta ce tana ci gaba da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa ranar 15 ga watan Nuwamba domin zaɓen sababbin shugabanni, abin da ɓangaren Wike ke adawa da shi wanda ya sa har suka kai jam’iyyar kotu.
