Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano Hashimu Dungurawa ya sanar da korar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji Abdulmumin Jibrin Kofa daga jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar ya sanar da hakan ne yayin ganawa da manema.
A cewar Hashimu Dungurawa jam’iyyar ta yanke hukuncin korar Abdulmin Kofa daga jam’iyyar bisa zargin aikata zagon ƙasa ga jam’iyya da kuma rashin biyan kuɗin jam’iyya.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Abdulmin Kofa ya bayyana goyon bayansa ga shugaba Tinubu a zabe mai zuwa, tare da sanar da cewa zai iya barin jam’iyyar NNPP a duk lokacin da yake so.
