Hukumar jirgin ƙasa ta kasa NRC ta ce ta kammala gyare-gyare a hanyar dogon Abuja-Kaduna, inda ta ce jirgin zai koma aikin jigilar fasinja a hanyar a mako zuwa.
A ranar 26 ga watan Agusta ne dai jirgin ya tuntsure, inda wasu mutane da dama suka samu raunuka, lamarin da ya sa aka dakatar da aikin jirgin domin a yi gyara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Callistus Unyimadu ya fitar, ya ce hukumar ta yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da kammala gyare-gyaren cikin tsanaki.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana asalin ranar da jirgin zai koma aiki ba, inda ya ce, “nan da kwanaki kaɗan za a bayyana asalin ranar da za a fara jigila.