Jam’iyyar NNPP ta nesanta kanta daga tsohon dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sakamakon kalaman da ya yi kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC.
A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a ranarLahadi a Legas, Sakataren Yada Labaran jamiyyar tsagin dake adawa da Kwankwaso, Dakta Oginni Olaposi, ya nemi afuwa ga Shugaba Tinubu da APC bisa abinda ya kira kalaman batanci da cin zarafin da Kwankwaso ya yi masa.
“Jam’iyyar ta kori tsohon gwamnan Jihar Kano daga cikinta kuma ta katse duk wata alaka da shi da kuma tafiyarsa ta Kwankwasiyya.
“Kwankwaso ba ya magana a madadin NNPP kuma bai kamata ya ci gaba da amfani da sunan jam’iyyar wajen sukar Shugaban kasa da jam’iyyar APC ba.
“Domin an kori Kwankwaso tun da dadewa, kuma ya kamata ya mai da hankali kan matsalolinsa, inda ya ce da dama daga cikin magoya bayansa sun koma jam’iyyar APC.” In ji Dakta Olaposi.
Sanarwar ta ambato hukuncin wasu kotuna da suka tabbatar da korar Kwankwaso daga jam’iyyar, ciki har da hukuncin Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) na ranar 3 ga Afrilu, da na wasu kotunan jihohi kamar Abia.
