Kasar Morocco dake karbar bakin gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON 2025, ta fara gasar da kafar dama, bayan lallasa kasar Comoros da ci 2 da nema.
Kasashen sun kara ne a wasan farko da suka buga daren Lahadi.
Dan wasa Ibrahim Diaz da El-kabi ne suka jefa wa Morocco kwallayen bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Sakamakon nasarar ta sa Morocco ta zamo kan gaba da naki 3 a rukunin A.
A rukunin B, Afirka ta Kudu za ta kara da Angola, yayin da Masar da Zimbabwe zasu kwace raini a daren yau Litinin
