
Mataimakin gwamna Kano Aminun Abdussalam Gwarzo a yayin mika sunaye da kuma bayanan ga gwamnan Edo
Gwamnatin jihar Kano ta mika sunaye da kuma bayanan mafarautan jihar 16 da aka kashe a Uromi ga gwamnatin jihar Edo.
Matakin na zuwa ne bayan kafa kwamitin bincike da gwamnatin Kano ta yi domin tantance gaskiyar lamarin da kuma gane wadanda abin ya shafa.
Gwamnatin Kano mika sunaye da bayanan iyalan ne ta hannun kwamiti mai karfi da ta kafa wanda ya kuma ziyaraci jihar Edo tare da mikawa gwamnan jihar a ranar Alhamis.
A yayin tarbar kwamitin, Gwamnan jihar Edo Sanata Okpebholo ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatinsa sun kafa kwamitin bincike domin gano hakikanin abin da ya faru dangane da kisan gillar da aka yi wa mafarautan daga Kano.
Gwamnan jihar ya kuma bayyana damuwar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan lamarin, inda ya ce shugaban na fatan ganin an samar da ingantaccen tsaro a dukkan sassan Najeriya, domin tabbatar da zaman lafiya da bunkasar kasuwanci.
Bayan mika rahoto, tawagar Kano da Gwamna Okpebholo sun ziyarci Uromi, inda suka gana da al’ummar Hausawa, suka jajanta musu tare da tabbatar da cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace.
Wannan ci gaba na nuna himmar gwamnatin Kano da ta Edo wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.