Ministan tsaro Mohammed Badaru Abubakar ya ajiye mukaminsa.
A cewar wata sanarwa daga fadar shugaban kasa da Bayo Onanuga ya sanya wa hannu ranar Litinin da daddare.
“Badaru ya yi murabus ne saboda dalilan rashin lafiya, kamar yadda ke kunshe a cikin wasikar da ya aike wa Shugaba Tinubu, kuma tuni shugaban ya amince da murabus ɗin. In ji sanarwar.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai aike da sunan wanda zai maye gurbin ministan ga Majalisar Dattijai domin tantancewa a cikin wannan makon.
