Shugaban gwamnatin da ke mulkin Sudan Abdel Fattah al Burhan ya ce ba za a taɓa samun zaman lafiya a Sudan ba sai an kawar da rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces (RSF).
Da yake magana da manema labarai a gidansa da ke Port Sudan ranar Lahadi, Burhan ya ce, “Ba za a samu zaman lafiya ba sai an kawar da RSF, kuma duk wata tattaunawar zaman lafiya da aka sanya RSF a cikinta, za ta jinkirta rikici ne kawai.
Burhan ya ƙara da cewa yaƙin da ake yi a ƙasar ya haddasa gagarumar ɓarna, wadda ta shafi fararen-hula da kuma gine-gine a faɗin ƙasar.
Ya ce babu wani ɗan ƙasar Sudan da yaƙin bai shafe shi ba amma duk da haka al’umar ƙasar sun haɗa kai wajen yaƙar ƙungiyar da ke tayar da ƙayar baya.
Yayin da yake magana kan ƙoƙarin ƙasashen duniya na wanzar da zaman lafiya, ya nuna ƙarin kiraye-kiraye da suke yi kan hakan bayan RSF ta ƙwace yankin Al Fasher a watan Oktoba, yana mai cewa matakin na zuwa ne a yayin da ake neman ganin rundunar ta faɗaɗa ikonta zuwa wasu yankuna.
