
Kylian Mbappe ya kafa wani tarihi a sabuwar ƙungiyarsa ta Real Madrid a inda ya ci jimillar ƙwallo 31 a kakarsa ta farko.
Mbappe ya zura ƙwallaye biyun da suka bai wa Madrid nasara kan Villareal da ci 2-1, A ranar Asabar ɗin makon jiya, wanda ya sa ƙungiyar ta kamo Barcelona a yawan maki, duk da Barca na da kwantan wasa guda.
Gwarzon ɗan wasan ya ci ƙwallo a minta na 17 da na 23, inda ya soke ƙwallon da ɗan wasan Villareal Juan Foyth ya fara ci tun a minti na 7.
Da waɗannan kwallaye da ya ci, Mbappe ya tara jimillar ƙwallaye 31 tun zuwansa Real Madrid cikin duka gasannin da ya buga, inda ƙwallo 20 ya ci su a gasar La Liga.
Cin ƙwallo 31 na nufin Mbappe ya haura yawan ƙwallaye 30 da tsohon gwarzon ɗan wasan Madrid Ronaldo Nazario ya ci a kakar 2002-03. Sannan kuma Mbappe ya kama hanyar doke tarihin ƙwallo 33 da Cristiano Ronaldo ya ci a kakar 2009-10.
Sai dai duk da wannan gagarumin matakin bajinta da ya kai, Kylian Mbappe wanda ɗan asalin Faransa ne, ya nuna ƙana’a inda ya ce kar a kai shi matsayin gwarazan Real Madrid, ko da ya haura su a wajen gwanintar cin ƙwallo.
Mbappe ya ce, “Su gwaraza ne da suka yi suna a zamaninsu. Yana da muhimmanci, amma abu ne kawai na ƙidaya. Idan na ci ƙarin ƙwallaye fiye da na Ronaldo da Cristiano, ba ya nufin na fi su, kawai hakan na nufin kakar wasana ta farko tana yin kyau.
“Muhimmin abu shi ne taimaka wa wajen cin kofuna. Cin ƙwallaye yana da alfanu, amma ko da hakan, abin buri shi ne idan muka lashe kofin LaLiga, da na Zakarun Turai, da Copa del Rey.”
Kylian Mbappe na da damar cin ƙarin ƙwallaye a wasa fiye da 10 da zai iya bugawa kafin ƙarewar kakar bana, a gasanni daban-daban da Real Madrid ke ciki.
Sannan zai iya ƙara cin wasu ƙwallayen a wasannin da zai buga wa tawagar ƙasarsa Faransa ranar Alhamis mai zuwa, wanda zai ƙara masa jimillar ƙwallaye na shekara guda.
TRT