
Wasu‘yan bindiga da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai sansanin sojin Najeriya, ana kuma zargin sun kashe wasu sojojin da kuma kame wasunsu a jihar Borno.
Daily Trust ta rawaito cewa, ‘yan ta’addan sun kai harin ne a sansanin sojin na Forward Operation mai ɗauke da bataliya ta 153 da misalin karfe 3 tsakar daren Litinin
Ɗaya daga cikin majiyoyin da ya buƙaci sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa, mayaƙan na Boko Haram sun kuma yi garkuwa da wasu sojojin na Najeriya bayan sun raba su da muhallansu a yayin farmakin.
“Ƴan ta’addar sun kona tankunan yaƙi tare da awon gaba da tarin makamai daga sansanin sojin” a cewar majiyar tsaron da jaridar ta rawaito.
Ƙaramar Hukumar Marte na da tazarar kilomita 38 daga Ƙaramar Hukumar Dikwa a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.
A source in Dikwa told our correspondent that gunshots were heard, and a fighter jet of the Najeria Air Force was seen hovering the area.
Wata majiya a Dikwa ta shaida wa jaridar cewa an jiyo ƙarar harbe-harben bindiga an kuma ga jiragen yakin sojan saman Najeria na shawagi a yankin.