
Rahotanni sun ce Mayaƙan Boko Haram sun kashe aƙalla mutum 55 a arewa maso gabashin Najeriya a wani hari da suka kai kan wasu mutane da suka koma garinsu daga sansanin ƴan gudun hijira, kamar yadda kafar AFP ta ruwaito daga wani ma’aikacin ƙungiyar agaji.
Harin ya auku ne a daren ranar Juma’a a garin Darul Jama a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno, garin da ke tsakanin Najeriya da Kamaru.
Wata majiya ta shaida wa AFP cewa daga cikin waɗanda aka kashe ɗin guda 55, har da sojoji guda biyar, da kuma wani ɗan sa-kai guda ɗaya.
Mazauna yankin sun ce mayaƙan sun ƙaddamar musu da harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare, inda suka ce maharan sun kutsa garin ne a kan babura ɗauke da muggan makamai, inda suka fara harbe-harben kan mai uwa da wabi, sannan suka riƙa ƙone gidaje.
Wani wanda ya tsira mai suna Malam Bukar da ya tsere tare da iyalansa a cikin daren, ya bayyana wa AFP cewa da suka koma gida da safe, sun ga gawarwakin mutane aƙalla guda 55 a yashe.