
Gwamnatin Kano ta ce jihar Kano ce ta 18 cikin jihohin da su fara yin rijistar katin zabe ta Internet tun bayan da aka bude.
Kwamishinan ya da labarai da al’amuran cikin gida kwamaret Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana haka yayin da kwamitin wayar da kan al’umma kan rijistar katin zabe ya gana da kungiyar mawaka mawallafa na Kwankwasiyya ranar Laraba.
An yi ganawar ne domin neman hadin kan kungiyar mawallafa kan yadda za a wayar da kan al’umma dangane da yin rijistar katin zabe.
Waiya ya ce yayin ganawarsu da kwamishinan zabe na kasa reshen Kano ya fada musu a kewayan farko mutum dubu 5000 ne su ka fara abubuwan farko ma yin rijistar zabe ta Internet ( Free Registration).
Ya ce daga baya alkaluma sun kara fitowa cewa ‘yan Najeriya sama da miliyan 1.3 ne suka yi rijistar.
Sai dai ya ce abin takaici mutane dubu goma ne su ka yi a jihar Kano, wanda hakan ya sa ta a matsayi na 18 cikin jihohi 36.
Ya ce abin tashin hankali ne a ce kananan jihohi sun yiwa Kano fintinkau.
Kwamishinan yada labarai Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kara da cewa ya zama wajibi jihar Kano ta zama na daya wajen yin rijistar katin zabe.
Ya nemi hadin kai da gudunmawar kungiyar mawaka mawallafa na Kwankwasiyya domin wayar da kan al’umma kan yin rijistar katin zabe.
Ya ce rijistar zabe ta mutanen Kano ta kai miliyan shida a INEC sai dai kalubalen a yanzu shine ana so ta kai miliyan 10 kafin zaben 2027.
Da yake jawabi mai taimakawa gwamnan Kano kan harkokin Al’adu da Nishadi, Tijjani Gandu, ya ce za su yi aiki tuƙuru wajen wayar da kan al’umma kan rijistar zabe.
Ya ce a shirye suke su bayar da hadin kan da ya dace wajen samun nasarar sa.
Taron kwamitin da kungiyar mawallafan ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga gwamnatin Kano.