Shugaban Kamfanin Dangote ya bayyana cewa matatar mai ta Dangote na da isasshen fetur da zai wadatar da Najeriya gaba ɗaya.
Aliko Dangote ya fadi haka ne a ƙarshen mako, yana mai cewa matatar na da fiye da lita miliyan 500 na fetur a rumbunan ajiyar Mai wanda yawansa ya fi karfin abin da kasar ke bukata.
Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da direbobin manyan motoci masu dakon mai ke yajin aiki a Legas, suna zargin cewa jami’an ‘yan sanda na cin zarafinsu a titunan birnin.
Yayin wata tattaunawa da tawagar wakilai daga ƙasar Zambia, Dangote ya jaddada cewa manufar gina matatar ba wai don Najeriya kawai aka yi ba, sai dai don amfanin daukacin nahiyar Afirka.
“Anyi matatar ne domin Najeriya da kuma sauran kasashen Afirka baki ɗaya,” in ji shi.
