
Matatar mai ta Dangote za ta gina wani rumbun ajiya a ƙasar Namibiya domin adana ganga miliyan 1.6 na man fetur da dizel.
Matatar za ta ware wannan adadi ne domin sayarwa ga ƙasashen da ke kudancin Afirka.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyi na cewa za a yi amfani da rumbun wajen yin hada-hadar fetur a ƙasashen Botswana, da Namibiya, da Zambiya, da kuma Zimbabwe.
Haka kuma, Dangote na duba yiwuwar fara kai man fetur zuwa ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
A watan da ya gabata ne wata majiya ta bayyana cewa matatar Dangote ta fara sayar da mai zuwa nahiyar Asiya, karon farko da matatar ta yi hakan a wajen nahiyar yammacin Afirka.