Kamfanin man fetur na Ɗangote ya bayyana cewa gidajen mai da ke sayen fetur daga matatar sa za su fara sayar da litar fetur a kan N739 daga ranar Talata a jihar Lagos.
Shugaban kamfanin Alhaji Aliko Ɗangote ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin taron manema labarai a Lagos.
Dangote ya tunatar da jama’a cewa tuni kamfanin ya rage farashin fetur daga N828 zuwa N699.
“Sabon tsarin farashin na daga cikin kokarin da matatar Dangote ke yi na daidaita samar da man fetur a cikin gida.
Sabon farashin zai ya fara aiki ne daga ranar 11 ga Disamba, kuma shi ne karo na 20 da matatar Dangote ke sauke farashin fetur a wannan shekarar.
Ɗangote ya kuma ce, matatar Dangote ta kuduri aniyar tabbatar da cewa man fetur bai wuce N740 ba a fadin kasar nan a cikin watan Disambar da muke ciki da Janairun 2026.
Attajirin ya bayyana cewa sun yi haka ne domin sauƙaƙa wa jama’a wahalhalun rayuwa a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
