Matashiyar tana aiki ne da wasu gungun matasa su hudu a inda suke ta’annati a birnin Kano
Kakakin rundunar Abudullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da kame matashiyar mai suna Shamsiyya ranar Alhamis[
Kiyawa ya ce, ta shiga hannunsu ne tun 12 ga watan Disamba bayan shafe tsawon shekara guda ana farautar ta.
”Shamsiyya ta kware wajen bullo da dabarun yaudara daban-daban don hilatar mutane wajen sace musu wayoyi”, in ji sanarwar.
Ya kuma kara da cewa, Shamsiyya da ake zargin na aiki da wasu matasa hudu da ke taimaka mata ciki har da wani mai mashin mai kafa uku watau dan adaidaita sahu.
Wanda yake kwararre wajen cire wayoyi daga makulli, wajen gudanar da ayyukanta.
Sanarwa ta kuma kara da cewa, Shamsiyya kwararriyar mai yaudara ce da ke shiga gidajen matan aure tare da sace musu wayoyinsu da kuma yin amfani da wayoyin wajen sace musu kudade daga asusun ajiyarsu na banki.