
Sama da Matasa 3,600 ne suka yi rijistar shirin tallafawa matasa manoma a jihohin Arewa Maso Yamma, na gidauniyar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin.
Shugaban shirin Farfesa Bashir Muhammad Fagge ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da yay i da Premier Radio a ranar Talata.
“Shirin na da nufin bunkasa tattalin arzikin yankin ta hanyar karfafa harkar noma.
Za a raba tallafin noman ga wadanda suka ci gajiyar shirin kafin daminar bana domin su samu damar fara noma da wuri.” In ji shi.

Ya kuma ce, ana sa ran kammala tantance sunayen wadanda suka cika ka’idojin shiga shirin zuwa ranar 7 ga watan Afrilu.
Shirin na daga cikin matakan da gidauniyar ta dauka don rage rashin aikin yi da inganta harkokin noma a Arewa Maso Yamma.