Masu zanga-zanga a Kenya sun sha duka da hayaƙi mai sa ƙwalla bayan sun fito suna kan titinan neman kadin mutuwar wani fitaccen mai fafutika a ofisihin ‘yansandan ƙasar.
‘Yan zanga-zangar sun ce wasu matasa ɗauke da tsumagiya da makamai a kan babura ne suka ka far musu yayin zanga-zangar, suka kuma zargi ‘ƴansanda da zuba ido ana cin zarafinsu.
Tun da farko, jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin amfani da hayaƙi mai sa ƙwalla wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Ƴansanda a Kenya sun ce Albert Ojwang ya mutu ne sakamakon raunin da ya ji wa kansa, batun da masu shigar da ƙara suka musanta.
