
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ya ce a kai yiyuwar ’yan Arewacin kasar nan su tsayar dan takarar shugaban kasa da nufin yaƙar Tinubu a zaɓen 2027, saboda tsare-tsaren gwamnatinsa da suka jefa mazauna yankin cikin halin wahala.
Babachir David Lawal ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da shi aka yi a tashar Talabijin ta Trust TV, inda ya ce shugabannin siyasar Arewa a arewacin kasar nan na aiki tare da kungiyar kare muradun Arewa ACF da Kungiyar Dattawan Arewa NEF domin cin ma wannan manufa, kuma Babu yadda za a yi mutum ya ci zaɓe ba tare da samun goyon bayan waɗannan ƙungiyoyin ba.
Ya ƙara da cewa tsare-tsaren Tinubu ciki har da cire tallafin mai da tsadar rayuwa sun jefa ’yan kasar nan cikin matsanancin rayuwa, don haka shugabannin siyasar Arewa ke ƙoƙarin fito da ɗan takararsu a zaɓen da ke tafe.
Babachir ya kuma ce maimakon gwamnatin Tunibu ta maida hankali kan yadda zata saukaka wa al’umma halin da suke ciki, sai gwamnatin ta ɓige da ƙirƙiro abubuwan da ke ƙara jefa ’yan kasar nan cikin tsanani.