
Fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywood kuma tsohuwar matara Sani Danja ta tabbatar da mutuwar aurenta na biyu da wani dan kasuwa.
Mansurah ta bayyana haka ne a shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, inda aka tattauna da ita tare da Fati Mohammad tsohuwar jaruma a masana’antar, kan zargin matan Kannywood da rashin zaman aure.
Jarumar ta ce, mutuwar auren ya zo mata ne a wani yanayi na ba-zata,kuma kamar almara. Domin auren a wurinta na soyayya ne da kuma yadda mijin ya zo mata.
“Ni aure na yi na soyayya, domin “so makaho ne”, amma ashe mijin da wata manufar daban ya zo, ba aure na gaskiya ba”. in ji ta.
Jarumar ta zargi mijin da yaudararta da kuma tsere wa da kwangilolinta na miliyoyin naira.
A nata bayanin, Fati Mohammad ta ce, mutane na yi musu gurguwar fahimta, kuma ta kuma ce, yawanci ana auren matan Kannywood ne don sha’awa,
“Kuma kin san tunanin mata daban da na maza. Wani da an yi auren, da ya biya buƙatarsa sai ya sake ki. Ba za a yi tunanin shi ya sake ki ba, sai a ce kin ƙi zama saboda ‘ta saba da kuɗi.” In ji tsohuwar Jaruma Fati Mohammed.
An daura auren jarumar ne a cikin watan Yunin shekarar 2024 a wania salo nna ba-zata a inda aminiyarta Samira Ahmad ta bayyana labarin daura auren cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Instagram.
Samira ta wallafa ce: “Alhamdulillah, an daura auren Mansurah Isah yanzu. Allah Ya sanya alheri Ya ba su zaman lafiya. Amin.”
Daga baya ta sa bidiyon taron mata kewaye da Mansura da kuma isowar wasu maza a motoci a inda suka mika kudi a jakar leda da Samiran ke sanarwa cikin murna da cewa sadakin auren Naira Miliyan aka kawo.
Sai dai babu hoton mijin da kuma bayanin ko wanene shi.