Mambobin kwamitin gudanarwa na Hukumar Aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) sun rubuta takarda ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, suna neman ya cire shugaban hukumar.
A gefe guda kuma wasu kwamishinoni a Hukumar ta NAHCON) sun nemi shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, da ya yi murabus daga muƙaminsa, bisa zargin gazawa wajen tafiyar da harkokin hukumar.
Ɗaya daga cikin shugabannin gudanarwa na NAHCON, Abba Jatau Mala, ya bayyana kafar yaɗa labarai ta DCL cewa a baya kwamishinonin sun kafa wani kwamiti mai mambobi takwas, wanda ya tattara koke-koke tare da miƙa su ga shugaban ƙasa.
Sai dai a martanin da mai taimakawa shugaban NAHCON a ɓangaren yaɗa labarai, Ghali Sadik, ya musanta zarge-zargen da ake yi wa shugaban hukumar, ya bayyana cewa zargin ba su da tushe ballantana makama, yana mai jaddada cewa duk wanda ke tuhumar wani da laifi wajibi ne ya gabatar da gamsassun hujjoji.
A baya dai an zargi tsohon jami’i a hukumar, Jalal Arabi, da aikata almundahanar kuɗaɗe da ake zargin sun haura naira biliyan casa’in, lamarin da har yanzu ke ci gaba da ɗaukar hankali kafin barkewar wannan sabon rikici da ya shafi shugabancin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan.
