Malaman Kano Poly sun janye yajin aikin da suka tsunduma
Ahmad Hamisu Gwale
Ƙungiyar Malaman Kwalejin Fasaha ta kasa ASUP ta janye yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta fara, tare da umartar mambobinta su koma bakin aiki a ranar Litinin mai zuwa.
Shugaban ASUP, na kasa Shammah Kpanja, ne ya bayyana matakin janyewar a wata sanarwa da kungiyar ta fitar a 12 ga Disambar da muke ciki.
Kpanja ya ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU), tare da sharadin cewa za a sake yin wani taro a ranar 23 ga Janairu, 2025, domin kawo karshen takaddamar gaba daya.
Matakin na zuwa ne bayan tin da fari ASUP ta fara yajin aikin gargadi a ranar 2 ga watan Disambar da muke ciki sabida watsi da lamuran ilimin kwalejin a duka fadin kasa.
Kungiyar ta ce ta dakatar da yajin aikin ne bayan wani taro da aka gudanar tare da jami’an ma’aikatar kwadago da Ayyuka wanda aka cimma matsaya ta janye yajin aikin.